
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis, Hamas ta ce za ta tabbatar da ci gaba da aiwatar da abubuwan da ke ƙunshe a yarjejeniyar, ciki har da batun sakin waɗanda ta ke garkuwa da su a daida lokacin da aka tsara.
Kakakin ƙungiyar, Abdul Latif al-Qanoua ya tabbatar wa kafar yaɗa labarai ta Anadolu cewa ƙungiyar za ta saki waɗanda ta ke garkuwa da su muddin Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta.
Isra’ila dai ta saɓa yarjeniyoyin da aka ƙulla ta hanyar hana dawowar mutanen da rikici ya daidaita, da shigar kayakin agaji yankunan da ake bukata. Dalilin da ya sa al-Qanoua cewa muddin ƙasar ba ta mutunta yarjejeniyar da aka kulla ba, toh lallai babu musayar fursunonin da za a yi.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito wani shaidu daga Falasdinu na cewa, masu shiga tsakani sun bayyana cewa daga safiyar ranar juma’a, Isra’ila ta dauki alkawalin mutunta ka’idojin da aka gindaya yayin kulla yarjejeniyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI