Shugaban adinin kasar Iran Ayetullah Ali Hamaney ya bayyana cewa kasashen Larabawa hadi da Saudiyya ta taimakawa kasar Isra'ila sun ci amanar kasar Falasdin.
Hamaney, ya yada a Twitter inda yake sharhi akan matakan samar da daidaito a Falasdin inda yake kuma sukar irin rawar da kasashen larabawa ke takawa a cikin wannan lokaci akan matsalar ta Falasdin.
Hamaney wanda ya bayyyana hurda kasashen larabawa da gwamnatin Tel Aviv a matsayar cin amana ya kara da cewa,
"A yau wasu kasashen yankin gulf sun kasashe masu cin amana na karshe ga duniyar larabawa, sun ci amanar Falasdin, ko al'umman wadannan kasashen zasu amince da cin amanar da shugabaninsu ke cigaba da yi?"
Hamaney ya jaddada cewa yadda Saudiyya ke cigaba da kusanatar Isra'ila bai kasance ba face taimakawa manufar Amurka wanda yake cin amanar Falasdin"
Ya kara da kira da kar a amince da manufofin Amurka.