Babban Hafsan Hafsoshin Libiya Janar Mohammed Haddad da tawagar da ke tare da shi sun zagayi jiragen ruwan Turkiyya da ke aiki a gabar tekun Libiya.
A cikin sakon da aka sanya a adireshin Twitter na Ma'aikatar Tsaron Kasar Turkiyya, an bayyana cewa Haddad da tawagar da ke tare da shi sun ziyarci jirgin ruwan Turkiyya "TCG Gediz" a gabar tekun Libya a ranar 24 ga Agusta, 2021.
Jiragen na rangadi a yankin ne a matsayin wani bangaren tsaro na Rundunar Sojojin Ruwan Turkiyya.