Hadin gwiwar Rasha da China a kan wata

Hadin gwiwar Rasha da China a kan wata

An sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Rasha da China don kafa tashar hadin gwiwa ta sararin samaniya a kan wata.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Rasha (Roscosmos) ta fitar, an bayyana cewar an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Roscosmos da Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta kasar China (CNSA) don kafa tashar hadin gwiwa a kan wata don gudanar da bincike.

A cikin sanarwar wanda ya hada da bayanan cewa tashar za ta kasance wacce duk kasashe masu sha'awa zasu samu daman shiga, an bayyana cewa

"Haɗin kai tsakanin Roscosmos da CNSA zai ba da gudummawa don ƙarfafa haɗin hulɗar binciken kimiyya da kuma amfani da sarari samaniya don dalilai na lumana da za su amfani dukkan ɗan adam." 


News Source:   ()