Jami’ai a ƙasar sun ce babu ko da mutum guda da ya rayu a haɗarin da ya afku a birnin Sao Paulo.
Kamfanin jirgin saman da ya faɗi wato Voepass ya tabbatar da faruwar lamarin cikin daren jiya.
Mahukuntan a ƙauyen Valinhos da jirgin ya faɗi, sun ce iya mutanen da ke cikin jirgin haɗarin ya shafa, amma kuma ya lalata gidaje da sauran gine-ginen da ya faɗa kansu.
A nasa ɓangaren shugaban ƙasar ta Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya jajantawa al’ummar ƙasar kan faruwar lamarin, yana mai cewa sama bai ji dadin yadda zai sanar da faruwar baƙin labarin ba amma ya zama dole ƴan ƙasar su san cewa ƴan uwan su fasinjojin jirgin 58 da kuma ma’aikata biyu sun mutu.
Har yanzu dai babu cikakken bayani kan dalilin faɗuwar jirgin daga hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar, sai dai kuma faya-fayan bidiyo sun nuna yadda wasu sassan jirgin suka kama da wuta tun yana sama kafin daga bisani ya rikito.
Bayanai sun ce jirgin ƙirar Flightradar 24 wanda aka samar a shekaar 2010 na da matuƙar ƙarfi da kuma juriya wajen aiki, kuma an samar da shi ne a jihar Parana ta ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI