Gwamnatin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun yi musayar fursunoni

Gwamnatin Yaman da 'yan tawayen Houthi sun yi musayar fursunoni

A jihar Al-Dali da ke kudancin Yaman an saki fursunonin yaki 12 karkashin yarjejeniyar da gwamnati da 'yan tawayen Houthi suka kulla.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin soji sun bayyana cewa, an yi musayar fursunonin a gundumar Al-Arzal da ke yammacin jihar Al-Dali.

A karkashin musayar, an saki sojojin Yaman 6 da mayakan Houthi 6. Haka zalika an yi musayar gawarwakin sojojin gwamnati 24 da na mayakan Houthi 22 da aka kashe a arangamar da aka yi a yankin.

An bayyana cewa, shugabannin yankin ne suka taimaka wajen yin musayar fursunonin yakin.

 

 


News Source:   ()