Gwamnatin Trump za ta rage wa'adin visar dalibai 'yan kasashen waje

Gwamnatin Trump za ta rage wa'adin visar dalibai 'yan kasashen waje

An sanar da cewa gwamnatin Trump na shirin rage wa'adin yawan shekarun visa da ake baiwa daliban kasashen waje dake zuwa karatu Amurka zuwa shekaru hudu.

Kafafen yada labaran kasar ne suka yada cewa gwamnatin Trump ma shirin rage wa'adin visar dalibai 'yan kasashen waje dake karatu kasar da ma masu niyar zuwa karatu kasar zuwa shekaru hudu kachal.

Bukatar da ministan tsaron cikin gida ya nema, ma'aikatar harkokin waje ma ta nemi a rage yawan wa'adin visar dalibai da suka fito daga kasashen da ake goyon bayan ta'addanci zuwa shekaru biyu.

Dangane ga dokar yanzu daliban dake zuwa karatu a Amurka zasu iya zama kasar har sai sun kammala karatunsu.

Idan aka tabbatar da rage wa'adin visar, dalibai 'yan kasashen waje zasu rinka neman karin wa'adi ne idan basu kammala karatunsu cikin shekaru hudun ba, ko kuma suna da rashin lafiya ko kuma in sun samu wani dalilin zama kasar mai karfi.

Dangane ga sabon tsarin za'a rinka baiwa dalibai visa ne masu rukunan  ''F'', ''J'' ve ''I''

 


News Source:   ()