Gwamnatin Syria ta ce ƴantawaye sun amince su koma ƙarƙashin ma'aikatar tsaro

Gwamnatin Syria ta ce ƴantawaye sun amince su koma ƙarƙashin ma'aikatar tsaro

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce shugaban gwamnatin rikon kwaryar ƙasar Ahmed al-Sharaa ne ya cimma yarjejeniyar, a wata ganawa da yayi da jagororinsu, duk da dai sanarwar bata yi ƙarin haske kan lamarin ba.

 A makon da ya gabata ne dama firaministan ƙasar Mohammed al-Bashir, ya sanar da garanbalun da suke ƙoƙarin yiwa ma’aikatar tsaron ƙasar, ta yadda za a shigar da tsofaffin tawayen da kuma sojojin da suka yi Assad bore cikin rundunar sojin ƙasar.

Ko a ranar lahadin da ta gaba sai da akaji jagoran gwamnatin Syria Ahmed al-Sharaa, ya ce za su kwance ɗamarar mayaƙan ƴan tawayen ƙasar, tare da tabbatar da cewar dukkanin makamai na ƙarkashin kulawar gwamnati.

Wannan dai na zuwa ne makonni biyu bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad da ke samun mafaka  a Rasha da ƴan tawayen sukayi, bayan shafe shekaru da dama ana gwabza rikici a ƙasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)