Gwamnatin Siriya ta zargi Isra'ila da kai hari birnin Sham

Gwamnatin Siriya ta zargi Isra'ila da kai hari birnin Sham

Gwamnatin Bashar Al-Assad ta Siriya ta zargi Isra'ila da kai hari ta sama kan Sham Babban Birnin Kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Siriya SANA ya bayyana cewa, daga tsaunukan Golan, Isra'ila ta kai hari kan wasu matsugunan sojin Asad da ke kewayen Sham.

Ba a bayyana ko an samu asarar rai ko dukiya ba sakamakon harin.

An bayyana cewa "Garkuwar makamai masu linzami da mu ke da ita ta mayar da martani tare d lalata mafi yawan makanan da aka harba."

Isra'ila ba ta ce komai ba game da batun.

A Sham Babban Birnin Siriya akwai sojojin gwamnatin Asad da kuma 'yan ta'adda na haya 'yan kasashen waje da Iran ta ke daukar nauyin aiyukansu a kasar.


News Source:   ()