Gwamnatin Siriya, ta hanyar amfani da Rasha ta karya yarjejeniyar Dera da aka kulla a 2018, inda a shekara 1 da ta gabata ta kashe mutane 98 ta hanyar zaluntar su a yankin.
Mutanen 98 da aka kashe sun hada da wasu tsaffin sojojin gwamnatin Siriya 40 da suka bar aiki bayan fara yakin basasar kasar, sun shiga hannun gwamnati a lokacin da suka nemi da a yi sulhu a Siriya.
Ana ci gaba da tsare mutane da dama da suka nuna bukatar amfana da yarjjejeniyar tsagaita wutar ga gwamnatin Siriya.
Gwamnatin Siriya da masu goya mata baya, sun fara kai hare-hare ta sama a Dera da ke karkashin ikon 'yan adawa ta hanyar amfani da jiragen saman Rasha a watan Yunin 2018. Rasha da 'yan adawa masu dauke da makamai sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Dera a ranar 6 ga Yunin 2018.
A karkashin yarjejeniyar an tanadi za a iya yin afuwa ga duk wadanda suke son yin sulhu da gwamnatin Siriya.