Gwamnatin Asad ta yi amfani da makamai masu gubu har sau 17

Gwamnatin Asad ta yi amfani da makamai masu gubu har sau 17

Gwamnatin Bashar Assad a Siriya ta yi amfani da makamai masu guba a kalla sau 17, shugaban kungiyar sa ido kan makamai masu guba na kasa da kasa ya fada wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya bayan da kwararru suka binciki zarge-zarge 77 kan gwamnatin.

Fernando Arias ya kira lamarin "abu mai tayar da hankali" cewa shekaru takwas bayan mulkin Siriya ya shiga Yarjejeniyar Makamai masu guba, wanda ya haramta kera ko amfani da irin wadannan makamai, akwai tambayoyi da yawa da suka kasance akan ayyukan kasar da makamai masu guba.

Ya fada cewa kungiyar hana amfani da makamai masu guba ta (OPCW) za ta dauki sabon batun a shawarwarin da za ta yi da Siriya nan gaba - matakan sazu tabbata ne sabili da“kasancewar sabbbin makamai masu guba da aka gano a cikin samfuran da aka tattara a cikin manyan kwantenan ajiya a watan Satumbar 2020. ”

Arias ya ce ya aika da wasika yana sanar da gwamnatin Siriya cewa yana da niyyar aikawa da kungiyar OPCW don su duba batun daga 18 ga Mayu zuwa 1 ga Yuni, kuma ya nemi biza amma bai samu amsa ba. Ya ce ya sanar da Damascus yana jinkirta zuwan zuwa ranar 28 ga Mayu.


News Source:   ()