An bayyana cewa akallan farar hula hudu da suka hada da yara biyu sun rasa rayukansu tare da kuma raunanan wasu yara biyu sanadiyar wani harin da dakarun gwamnatin Bashar Asad suka kai a gundumar arewa masu yammacin Idlib.
Linzamin da dakarun suka harba da zummar ya afkawa wata motar da take dauke da farar hula a kauyen Jisr-Esh-Shugur, ya fada a yankin zaman lafiya kamar yadda jami’an White Helmets suka shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu.
An dai garzaya da yara biyun da suka samu munanan raunuka zuwa asibiti cikin gaggawa.
Yankin zaman lafiya ya kasance yankin da Turkiyya da Rasha suka amince ba za’a kai farmakai ba, amma dakarun Asad na ci gaba da sabawa wacannan yarjejeniyar inda suke cigaba da kai hare-haren kin kari akan farar hular yankin.