Gwajin allurar riga-kafin Covid-19 kan 'yan shekaru 12 zuwa 17

Gwajin allurar riga-kafin Covid-19 kan 'yan shekaru 12 zuwa 17

Kamfanin samar da magunguna na kasar Amurka mai suna Johnson & Johnson (J&J) ya fitar da sanarwar cewa sun kara ‘yan shekaru 12 zuwa 17 a gwajin allurar riga-kafin sabon nau'in kwayar cutar corona (Covid-19).

A cewar sanarwar da kamfanin ta fitar, an bayyana cewa gwajin asibitin na a mataki na 2 kuma za a fara gwajin allurar riga-kafin a kan masu aikin sa kai tsakanin shekaru 16 zuwa 17, sannan za a gudanar da gwajin kan ‘yan kasa da haka har zuwa 'yan shekaru 12.

A cikin sanarwar an yi nuni da cewa Covid-19 na da matukar tasiri ga ilimi, lafiyar hankali da yanayin zamantakewar al'umma gami da matsalolin rashin lafiya a tsakanin matasa.

Sanarwar ta ce "Yana da muhimmanci mu samar da alluran riga-kafi ga kowa da kowa, a ko'ina, don taimakawa wajen yaki da yaduwar kwayar cutar da nufin komawa ga rayuwar yau da kullunm.” 


News Source:   ()