Guterres ya yi kira ga Isra’ila da Falasdinu da su hanzarta kawo karshen “zubar da jini mara ma'ana"
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres ya yi kira ga Isra’ila da Falasdinu da su hanzarta kawo karshen “zubar da jini mara ma'ana, ta’addanci da barnar” da suke aikatawa tare da komawa akan tattaunawa domin sasantawa yadda za'a samar da kasa biyu.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi taro a karo na uku don tattaunawa kan tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinu da kuma harin sama da aka kai a Gaza.
Da yake jawabi ga majalisar, Guterres ya ce, mutuwa da halakar da aka yi a Gaza da Isra'ila suna lalata shirin fatan zama tare da zaman lafiya don haka ya kamata a kawo karshen rikice-rikicen nan take.
Antonio Guterres ya kara da cewa,
"Ya kamata bangarorin sun daina kaiwa juna hari da roka a gefe guda, da kuma ruwan bama-bamai ta sama a dayan bangaren nan take"
Da yake bayyana cewa Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tattaunawa da dukkan bangarorin don tsagaita wutar, Guterres ya bayyana cewa yana matukar kaduwa da mutuwar fararen hula Falasdinawa, da suka hada da mata da kananan yara, a Gaza, kuma ya yi nadamar mutuwar Isra’ilawa saboda rokokin da aka harba daga Gaza.
Sakatare Janar din ya yi gargadin cewa idan rikice-rikice suka ci gaba, za a iya samun matsalar tsaro da ba za a iya shawo kanta ba.
Da yake nuna cewa lalata ofisoshin 'yan jarida a Gaza abin damuwa ne matuka, Guterres ya kara da cewa,
"Ya kamata a bar 'yan jarida suyi aiki ba tare da tsoro ko cin zarafinsu ba"
Ina mai kira ga Isra'ila da Falasdinu da su hanzarta kawo karshen wannan "zubar da jini mara ma'ana, ta'addanci da barnata dukiyoyi" tare da mutunta dokokin kasa da kasa da na kare hakkin dan Adam, in ji Guterres.
A karshe ya bayyana cewa,
"Hanya guda kawai da ake da ita ita ce komawa ga shawarwarin kasa da kasa don samar da kasa biyu, dangane da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya masu dacewa, da dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyoyin da suka gabata, ya kamata a tabbatar da Kudus a matsayar babban birnin kasashen biyu cikin aminci da tsaro.