Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres ya bayyana rikicin arewacin Ethiopia a matsayin lamari mai tayar da hankali inda ya yi kira da a bude kofar kaiwa farar hula gudunmowa.
Guterres, wanda ya ja hankali akan irin masifar dake faruwa a yankin Arewacin Ethiopia ya yi kira ga dukkanin bangarorin dasu mutunta dokokin kasa da kasa.
Sakatare Guterres, ya bayyana cewa "Muna bukatar a bude kofar kaiwa farar hula dauki, ya zama wajibi a kai taimako a yankunan da ake rikicin"
A yayinda aka tamabyi Guterres akan yiwuwar Amurka za ta bayyana kungiyar Houthi dake Yaman a matsayar 'yar ta'adda, ya bayyana cewa matakin gefe guda ba zai haifar da da mai ido ba. Bai kamata mu tayar da kura ba a wannan lokacin.