Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Iraki

Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Iraki

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (UN), Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin bam din da aka kai a wata kasuwa a Iraki.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Sakatare Janar din ya fitar, an bayyana cewa Guterres ya yi Allah wadai da mummunan harin da ya nufi fararen hula, sannan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, gwamnati da kuma mutanen Iraki.

Sanarwar da ta lura cewa ya kamata a gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan harin da wuri-wuri, ta ce, "Wannan mummunan harin da aka kai kafin Sallar Eid-al-Adha yana tunatar da dukkan mu kan cewa annobar ta'addanci ba ta da iyaka."

Mutane 30 sun mutu kuma wasu 60 sun samu raunuka a fashewar da ta afku a kasuwar Al-Vahilat da ke yankin Sadr na Baghdad, babban birnin Iraki, a jajibirin Sallah.


News Source:   ()