Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar, ba a yin adalci wajen rarraba alluran riga-kafin cutar Corona (Covid-19) a duniya.
Ya ce "An kai kaso 75 na alluran riga-kafin da aka samar a duniya zuwa kasashe 10 kawai, sama da kasashe 130 ba su samu ko da allura 1 ba."
Guterres ya kuma ce, ba a yin adalci wajen rarraba alluran riga-kafin ga kasashe, kuma idan cutar ta yadu kamar wutar daji, tana sauna kama, to za ta iya kashe mutane da dama a lokaci guda.
Guterres ya ci gaba da cewa, duniya na bukatar tsarin riga-kafi na bai daya, kuma yana kira ga kasashen G20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da su aiwatar da tsarin riga-kafin na bai daya.