Cibiyar da ke kula da annobar guguwa ta Amurka ta ce, guguwar ta Milton dai na gudun mil 120 a kowace sa’a guda, a kusa da garin Siesta Key.
Haka nan ci biyar ta ce mahaukaciyar guguwar ta haifar da ambaliyar ruwa a yankin Tampa Bay da suka hada da biranen Tampa da St. Petersburg da Clearwater.
Mahaukaciyar guguwar Milton ta isa tsakiyar jihar Florida a yau Alhamis. © Rebecca Blackwell / APGwamnan jihar ta Florida Ron DeSantis ya ce guguwar Milton ta kuma yi barna a wasu kananan hukumomi da dama, inda ya ce ta lalata gidaje kusan 125, mafi yawancinsu gidaje ne na tafi da gidanka.
Ana sa ran guguwar za ta tsallaka gabar tekun Florida cikin daren yau, ta kuma kutsa cikin Tekun Atlantika, ganin cewa har yanzu guguwar na da ƙafin gaske.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI