Guguwar Laura ta yi ajalin mutane 3 a Amurka

Guguwar Laura ta yi ajalin mutane 3 a Amurka

Guguwar Laura da ta taso daga kudancin Amurka, gaba da tekun Mekziko kuma ake sa ran za ta bugi jihohin Texas da Louisiana ta shiga mataki na 4.

Hukumar Kula da Afkuwar Guguwa ta Amurka ta sanar da cewar guguwar Laura "Na da hatsari matuka gaya" a saboda haka ta gargadi jama'a.

Guguwar na tafiyar kilomita 225 a kowacce sa'a, kuma ana sa ran za ta bugi yankunan jihohin Texas da Lousiana.

An bayar da gargadin kar ta kwana a jihohin Lousiana, kudu-masu gabashin Texas da Mississipi. Sakamakon mamakon ruwan sama koguna sun cika makil a Louisiana da Texas.

Mahukunta sun yi gargadi cewar igiyar ruwa na iya zuwa nisan kilomita 50 a kan tsandauri sakamakon karfin guguwar.

An bukaci da a kwashe mutane rabin miliyan da ke Texs da Louisiana.

Rahotanni sun ce mutane 3 sun mutu sakamakon guguwar.


News Source:   ()