Guguwar Isaias da ta faro daga tekun Atlas ta isa ga gabar tekun jihar North Carolina da ke Amurka.
Guguwar mai karfin lamba ta 1 ta bugi yankin wajen shakatawa na Ocean Isle da kudancin jihar North Crolina da ke Amurka.
A lokacin da guguwar ta isa yankunan da babu ruwa, an samu mamakon ruwan sama da iska mai karfi a jihohin North Carolina da South Carolina.
Guguwar na gudun kilomita 135 a awa daya, kuma an bayar da gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohin arewa maso-gabashin Amurka da suka hada da Virginia da Maryland.
Haka zalika an aiyana dokar ta baci a jihohin North Carolina da New Jersey sakamakon guguwar.