Guguwar Helene ta yi ɓarna a Amurka

Guguwar Helene ta yi ɓarna a Amurka

Guguwar da aka yiwa suna Helene ta afkawa yankin Big Ben da misalin karfe 11 da minti 10 agogon Amurka, ko kuma karfe 3 da minti 10 agogon GMT, inda ta haifar da rudani wajen tintsirar da kwale kwalen dake gabar ruwa da kada itatuwa da kuma tafiya da motoci bayan mamaye tituna.

Gwamnan Florida Ron DeSantis ya tabbatar da mutuwar mutane 2, kamar yadda Gwamnan Georgia Brian Kemp shi ma ya ce mutane 2 sun mutu a jiharsa, yayin da tashar talabijin ta ABC tace wani ma'aikacin agaji ya mutu bayan da itace y afada a kan sa.

Rahotanni sun ce 'yan sanda da jami'an kashe gobara sun yi nasarar kwashe dubban mutane daga yankunan da ke da hadari, cikin su harda Atlanta.

Karfin guguwar ya sa tana tafiyar kilomita 225 a cikin awa guda, abinda ke bata damar kawar da duk abinda ta ci karo da shi.

Hukumar kula da yanayi ta gabatar da gargadi ga mazauna jihohin Georgia da South Carolina da North Carolina da su zauna cikin shiri safiyar yau.

Tashoshin jiragen sama a Tampa da Tallahasse da St Petersberg duk sun daina aiki tun jiya alhamis, ya yin da aka soke sauka da tashin daruruwan jirage a Charlotte da ke North Carolina da kuma Atlanta.

Gidaje sama da miliyan 4 da wuraren kasuwanci suka rasa wutar lantarki a Florida da Georgia da Carolina, ya yin da wasu dubai ke fuskantar irin wannan barazana a Virginia da Tannesse da Kentucky.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)