
Guguwar ta afku ne a ranar Juma’a, inda ta nausa arewacin tsibirin tekun Indiya da ke gabashin Madagascar, tare da lalata ruwan sha ga yawancin mazauna yankin.
Bayanai sun ce, guguwar ta faro ne daga kudu maso yammacin tsibirin a cikin 'yan sa'o'i ƙalilan.
An gano gawar wani mutum a maƙale a ƙarƙashin wata bishiya a birnin Saint-Denis, a cewar hukumomin Faransa.
Sauran waɗanda abin ya rutsa da su, mata biyu da namiji guda, ana zargin ambaliyar ruwa ce ta yi awun gaba da su, inda suka makale a karkashin laka, abin da ya sanya ma, hukumomi ke kyautata zaton lantarki ce ta yi ajalin nasu.
Kimanin mutane 160,000 ne har yanzu ba su da wutar lantarki, yayin da fiye da 950 ke zama a cibiyoyin kwana na wucin gadi da aka ware musu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI