Mutane 4 sun rasa raykansu sakamakon guguwar Alex da ta kunna kai Faransa.
Tun 1 ga watan Oktoba guguwar Alex ta addabi cikin garin Nice na kudancin Faransa, kuma ta janyo ambaliyar ruwa.
Guguwar mai gudu kilomita 186 a awa daya ta tsananta a kwanaki 2 da suka gabata, kuma Hukumar Kula da Yanayi ta rage yawan wuraren da ke da hatsari daga 11 zuwa 6.
Jami'an kashe gobara na yankin Alpes-Maritimes sun bayyana mutuwar mutane 4 tare da jikkata a kalla 20 sakamakon guguwar, kuma sadarwa da wasu kauyuka 3 ta yanke baki daya.
guguwar da ta janyo karyewar gadoji da dama, ta kuma janyo asarar dukiya da yawa.