Mutane 6 sun rasa rayukansu, an kwashe dubunnan daga matsugunansu sakamakon guguwar Gamma da ta mamayi wani bangare na kudancin Mekziko.
Mahukuntan kasar sun ce guguwar ta janyo iska mai karfi a gabar tekun Tsibirin Yujatan da kuma tsakanin jihohin Tabasco da Chiapas.
Sanarwar da Hukumar Kare Fararen Hula ta Mekziko ta fitar ta ce sakamakon zaftarewar kasa da guguwar ta janyo a Chiapas mutane 6 da suka hada da yara kanana 2 sun mutu.
Sanarwar ta ce an kwashe mutane dubu 500 daga Tsibirin Yujatan da wasu yankunan Chiapas, kuma sama da mutane dubu 3,400 aka kwashe daga Tabasco.