Dubunnan mutane sun taru a birnin Peshawar da ke Pakistan don nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu.
A cikin shirin nuna goyon bayan da Jam'iyar Cemaat Islami ta shirya a birnin Peshawar, an kafa tutocin Falasdinu, masu zanga-zangar sun sanya sakonnin nuna goyon baya ga Falasdinu kan alluna da suka dauka kuma suka rera taken adawa da Isra'ila.
Jam'iyyar a baya ma ta gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu a babban birnin Islamabad da birinin Karachi.