Tuni aka ga fuskokin manyan shugabanni irin Xi Jinping na China da Narendra Modi na India da kuma Recep Tayyib Erdogan na Turkiya a wannan taro, wanda ya tattaro wakilai da jami’an diflomasiyyar ƙasashe mambobin BRICS da kuma waɗanda ke shirin shiga ƙungiyar.
Taron dai shi ke matsayin mafi tattara jama’a da Rasha ta jagoranta a cikin ƙasarta tun bayan faro mamayarta a Ukraine cikin watan Fabarairun shekarar 2022, a wani yanayi da Moscow ke fatan ƙarfin tattalin arziƙin ƙungiyar ta BRICS ya sauya tafiyar da duniya ta ke ka a halin yanzu ƙarƙashin tsare-tsaren ƙasashen yammaci.
Samun sabbin mambobi ga ƙungiyar ta BRICS na daga cikin manufofin Rasha da ke fatan faɗaɗa ƙungiyar wadda ta faro a baya da iyakar ƙasashen Brazil da Rasha da India da China da kuma Afrika ta kudu.
Bayanai sun ce manyan batutuwan da taron na BRICS zai tattauna akwai shirin ficewa daga tsarin hada-hadar kuɗi na SWIFT wanda Rasha ta fice daga ciki tun a shekarar 2022 baya ga lalubo hanyar yayyafa ruwa a rikicin gabas ta tsakiya.
Yayin taron, Putin zai yi kebantacciyar tattaunawa da Modi na India baya ga Xi na China daga bisani sannan Ramaphosa da al-Sisi shugabannin Afrika ta kudu da Masar dukkaninsu a yau Talata sai kuma ganawarsa da Erdogan na Turkiya da kuma Masoud Pezeshkian a gobe Laraba.
A ɓangare guda Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres zai yi tattaki zuwa Rasha don halartar taron, karon farko tun watan Aprilun 2022 inda bayanai ke cewa zai yi tattaunawa ta musamman da shugaba Vladimir Putin a gobe Laraba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI