A ƙalla hecta dubu 1 da 182 ne gobarar ta ƙona kamar yadda hukumomi suka tabbatar a Amurka.
Gidaje da yawa sun ƙone sakamakon gobarar dajin kuma gwamman masu kashe gobara ne suka duƙufa domin dakatar da wutar da ke ci babu ƙaƙƙautawa.
Tuni aka tseratar da mutum dubu 30 sakamakon tsanantar gobarar daji a yankin Pacific Palisades dake maƙwaftaka da Los Angeles da California.
Hukumomi sun yi gargaɗin kan cewa akwai wata iska mai ƙarfin gaske dake tafe da daddare, kuma za ta iya ƙara ta’azzarar girman gobarar.
Da zarar iskar mai ƙarfi ta zo, to hakan zai tirsasawa mutane da ke rayuwa a gidaje kusa da inda iftila’in ya shafa barin muhallansu.
01:21Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies
Amince Zabin son raina Gobarar daji a Los Angeles REUTERS - Mike BlakeLabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI