Gobarar da iska ke rurawa ta tursasa kwashe mutum dubu 31 saboda irin barazanar da ta ke yi ga rayuwar jama' a a yankin.
Wutar dajin da ke ci a Los Angeles tun a farkon watan Janairu ta tursasa ma’aikatan kwana-kwana a yankin aiki babu ji babu gani, inda suka shawo kan wutar a manyan yankuna biyu da ta fi yiwa illa a tsakiyar birnin na Los Angeles.
Cikin ƴan awanni ne dai wannan wuta da ta tashi ta yi mummunar barna da ta kai kwatankwacin biyu bisa uku na wadda aka gani a ranar 7 ga watan Janairu na shekarar 2025.
An tirsasawa mutum dubu 31 barin muhallansu sannan akwai yuwuwar wasu mutum dubu 23 su fice daga muhallansu a nan gaba saboda barazanar wutar kamar yadda babban jami’in tsaron yankin Los Angeles Robert Luna ya tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI