Gobarar daji ta barke a Siriya bayan harin da gwamnatin Assad ta kai

Gobarar daji ta barke a Siriya bayan harin da gwamnatin Assad ta kai

Bayan hare-haren da gwamnatin Bashar Assad ta kai a Siriya, gobarar daji ta barke a yankin tsaunin Turkmen da ke arewacin lardin Latakia.

Bayan gwamnatin Asad da kungiyoyin 'yan ta'adda masu samun goyon bayan Iran sun kai hari kan yankin tsaunin Turkmen da makamai, gobarar daji ta barke a yankin daji kusa da kauyukan Sellor da Kelez cikin dare.

Galibi an shawo kan gobarar tare da sa hannun mutanen yankin da ruwan saman da ya fara da sanyin safiya.

Ana ci gaba da aiyukan kashe gobarar, wacce ke ci gaba a wasu yankuna.


News Source:   ()