Gobarar "Caldor" ta sanya ayyanar da dokar ta baci a jahohin Calfonia da Nevada a Amurka
An ayyana dokar ta-baci a jihohin California da Nevada saboda gobarar "Caldor", wacce ta fara ranar 14 ga watan Agusta a yammacin Amurka.
A California, hukumomi sun ba da sanarwar cewa an yi nasarar kashe kashi 20 cikin 100 na wutar.
Yayin da sama da murabba'in kilomita 800 suka lalace a gobarar, an nemi mutane dubu 53 da su fice daga yankin.
Gwamnonin California da Nevada sun ayyana dokar ta baci yayin da gobarar ta bazu cikin sauri a yankunan.
Ganin cewa sama da gidaje 490 da wuraren aiki 12 sun lalace a gobarar, mahukunta sun yi gargadin cewa karin gine -gine dubu 34 na cikin hadarin rugujewa.