Akalla mutane 15 sun mutu sannan da dama sun ji rauni a gobarar da ta tashi a wata masana'anta da ke samar da magungunan kashe kwayoyin cuta a Indiya.
Gobarar ta tashi a wata masana'anta da ke samar da magungunan kashe kwayoyin cuta a Pune, Maharashtra.
Wutar ta yadu cikin sauri sanadiyar kamawar da wuta da sinadaran suka yi.
Yawancin ma'aikatan kashe gobara da aka aike zuwa wurin sun yi kokarin kashe wutar.
Bayan shafe awanni ana kokarin kashe wutar an yi nasarar kashe wutar.
Bayan an kashe wutar, an sanar cewa a kalla mutane 15 sun mutu sanadiyar ibtila'in.
Mahukunta sun sanar da cewa galibin wadanda suka mutu a gobarar hayaki ne ya turnukesu.