Mutum 7 sun rasa rasa rayukansu sanadiyar gobarar da ta afku a gidan tsofaffi dake yankin Tumen dake kasar Rasha.
Ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta sanar da cewa, gobara ta afku a gidan tsofaffi dake kauyen Borovskiy dake yankin Tumen.
A sanadiyar gobarar mutum 7 sun rasa rayukansu inda kuma wani daya ya raunana.
An dai yi nasarar dakatar da gobarar inda kuma aka fara bincike akan lamarin.
AN dai kame wanda ke da gidan tsofafffin kasancewar bai da lasisi kuma ya na amfani da wani gida ne da bai dace ba.
Mutane 11 ne suka rasa rayukansu a gobarar da ta tashi a ranar 15 ga watan Disamba a gidan kula da tsofaffi a kauyen Isbuldino a Jamhuriyar Bashkortostan, Rasha.