An samu fashewar abubuwa a ma'ajiyar makaman sashin sojoji dake gundumar Bayzakov a lardin Jambyl a kudancin Kazakhstan.
Ma'aikatar tsaron Kazakhstan ta sanar da cewa fashewar a ma'ajiyar makaman sashin sojoji ta faru ne da misalin karfe 19.00 agogon kasar.
A cikin sanarwar an bayyana cewa,
"Gobara ta tashi kusa da daya daga cikin rumbunan rundunonin soji dake gundumar Bayzakov na lardin Jambil. Daga nan gobarar ta haifar da fashewar abubuwan da ba a sani ba a daya daga cikin rumbunan. Ana ci gaba da aikin kashe gobara a yankin."
Da yake jaddada cewa ana binciken musabbabin tashin gobarar ya kara da cewa an tura wani kwamiti na musamman karkashin jagorancin mataimakin ministan tsaron Kazakhstan Ruslan Shpekbayev zuwa yankin.