An sanar da cewa sansanin da Musulmin Rohingya ke fakewa dake kusa da birnin New Delhi a kasar Indiya ya kama da wuta lamarin da ya yi sanadiyar konewar rumfuna 56.
Kamar yadda jaridun Indiya suka rawaito, jami'in 'yan sanda R.P. Meena ya bayyana cewa gobara ta tashi a sansanin Musulmin Rohingya da ke kusa da tashar jirgin kasa a Kalindi Kunj a kudu maso gabashin New Delhi.
Da yake bayyana cewa rumfuna 56 inda aka tsugunar da kimanin 'yan gudun hijirar Rohingya 270, ta cinye da wuta ya kara da cewa babu wanda ya raunana.
Ya kara da cewa:
"Ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba kuma ana daukar matakan da suka dace." Meena ya bayyana cewa an yi nasarar kashe gobarar.