
Gobarar ta faru a lokacin da Otal-Otal ke cika a yankin sakamakon hutun tsakiyar zankon karatun da aka yiwa ɗalibai.
Ministan lafiya na Turkiyya Kemal Memisoglu ya ce mutum 1 daga waɗanda suka samu raunuka a gobarar na cikin mummunan yanayi, an kuma sallami mutum 17 daga cikin mutum 51 da suka jikkata bayan likitoci sun duba lafiyarsu.
Wutar ta tashi da ƙarfe 3 da mintuna 30 na tsakar dare agogon ƙasar a ɓangaren dafa abinci na Otal ɗin kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Tuni gwamnatin Turkiyya ta naɗa mutum 6 da za su jagoranci bincike kan musabbabin gobarar da ta kashe mutum 66 da jikkata 51 a ƙasar.
A lokacin da gobarar ta tashi Otal ɗin na ɗauke da baƙi 234, kuma mutum 2 ne suka mutu sakamakon tsalle da suka yi daga Otal ɗin da nufin fitowa lokacin da gobarar ta tashi.
Ministan cikin gida na Turkiyya Ali Yerlikaya ya ce aƙalla mutum 51 ne suka jikkata sakamakon bala’in gobarar da ta ƙone Otal ɗin Kartal a lardin Bolu da ke da tazarar kilomita 300 zuwa babban birnin ƙasar ta Turkiyya Istanbul.
Muna cikin tsananin damuwa. Mun rasa rayukan mutane 66 sakamakon gobarar da ta mamaye wannan Otal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI