Gobara ta kama wasu asibitocin da ake jinyar masu fama da Covid-19 a Rasha

Gobara ta kama wasu asibitocin da ake jinyar masu fama da Covid-19 a Rasha

An sanar da cewa kamawar gobara a wani asibitin da ake jinyar marasa lafiya masu dauke da kwayar cutar coronavirus a garin St. Petersburg dake kasar Rasha ta yi sanadiyar rayuka biyar.

Wuta ta kama ne a bene na shidda na asibitin Azizi Yorgi dake garin St. Petersburg.

Wutar dake da alaka da na'urar taimakawa numfashi ya yi sanadiyar rayuka biyar.

Daga asibitin an kwashe mutum 150 an kuma yi nasarar kashe wutar.

Tuni dai an fara bincike akan lamarin inda aka fara bayyana cewa wutar ta samu asaline daga na'u'rorin taimakawa numfashi wadanda suka lalace.

A kwanaki biyu da suka gabata a garin Krasnogorsk kamawar wutar a wata asibitin da ake kula da marasa lafiya mutum tara sun hallaka.

A makon jiya kuma kamawar wuata a wani asibitin dake Moscow inda ake jinyar marasa lafiya masu fama da Covid-19 mutum daya ya rasa ransa.

 


News Source:   www.trt.net.tr