Gobara ta kama a kusa da fadar firaiminista a Paris, babban birnin Faransa.
A cewar labaran da jaridun kasar suka rawaito, gobara ta tashi a kan rufin wani gini dake kan titin Varenne inda fadar Matignon woto ginin firaiministan Faransa da Ofishin Jakadancin Italiya da ke Paris suke.
Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa babu wanda ya ji rauni a lamarin.
An dai yi nasarar kashe gobarar.