Gobara ta tashi a Sansanin Sharya, inda bakin hauren Yazidi ke zaune a garin Duhok da ke arewacin Iraki.
A cewar bayanan da aka samu daga shaidun gani da ido, tantuna 130 sun lalace a gobarar da ta tashi ba tare da wani dalili ba a Sansanin na Sharya.
An bayyana cewa ‘yan kwana-kwana sun isa yankin kuma an fara aikin kashe gobarar.
Ba a fitar da wani bayani kan ko an samu asarar rayuka a gobarar ba.