Ministan Mai na kasar Iran Bijen Namdar Zengene ya bayyana cewa, gobarar da ta tashi a matatar man da ke kudancin babban birnin kasar Tehran a jiya ba ta cutar da sassan da ake hakon man ba.
Da yake magana da kafofin yada labarai na Iran, Zengene ya yi bayanai game da gobarar da ta tashi a matatar mai ta Shahada Tondguyan da ke kudancin Tehran.
Zengene ya kara da cewa,
"Wutar da ta kama matatar ba ta kama wuraren da ake sarrafa mai ba, rukunin samarwar bai lalace ba. Ana ci gaba da kashe wutar a wasu sassan matatan"
Ministan ya bayyana cewa ana sa ran wutar za ta ci gaba har sai an gama amfani da hydrocarbons a cikin tankokin biyu.