Mutane 8 sun rasa rayukansu, wasu 170 sun jikkata sakamakon gobarar da ta kama wata cibiya da ake tsare da 'yan gudun hijira a Sana Babban Birnin Yaman.
Daraktar Hukumar Yaki da Gudun Hijira ta Duniya Reshen Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya Carmela Godeau ta bayyana kamawar gobara a cibiyar da ake tsare da 'yan gudun hijira da ke Sana.
Godeau ta ce, bayanan farko da aka samu sun bayyana mutuwar mutane 8 tare da jikkatar wasu 170 wadanda 90 daga ciki ke cikin mawuyacin hali.
Godeau ta shaida cewar ana kula da wadanda suka samu raunuka, kuma har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.