Mutane 41 sun rasa rayukansu sakamakon kamawar gobara a wani asibiti da ake kula da masu dauke da cutar Corona (Covid-19).
Rubutacciyar sanarwar da aka fitar daga Ma'aikatar Lafiya ta Iraki ta ce, a jihar Zikar da ke kudancin kasar ne gobara ta kama a Asibitin Imam Hussain da ake kula da masu dauke da cutar Corona.
An bayyana cewa, mutane 41 sun rasa rayukansu sakamakon kamawar gobarar da tukunyar iskar gas ta janyo.
Jami'an bayar da agaji sun bayyana cewa, an kashe gobarar.