Gobara ta kama a jihar Carlifornia ta Amurka kuma an kwashe mazauna garin na Santa Barbara.
An ba da umarnin ƙwashe mutane daga yankin lokacin da gobarar ta yi barazanar kone guraren zaman mutane a garin Santa Barbara.
Da kyar 'yan kwana-kwana suka gudanar da aiyukan kashe gobarar saboda yanayin garin kuma da iska mai karfi.
Yayin da ake ci gaba da kokarin kashe gobarar, hukumomi sun sanar da cewa an shawo kan rabin gobarar.
An bayyana cewa gobarar ta yi barazana ga gidaje 50 a yankin yayinda hekta 8 na dazuzzuka suka kone kuma wata ta lalace.