Mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a gidan kula da gajiyayyu da ke Yukren.
Sanarwar da aka fitar daga hukumar bayar da agaji gaggawa ta Yukren ta ce, gobarar ta kama da tsakar rana a gidan ajje gajiyayyun.
An bayyana mutuwar mutane 13 tare da jikkatar wasu 4 sakamakon gobarar.
Mahukunta sun ce, a lokacin da gobarar ta kama akwai mutane 33 a cikin ginin.
Ba a bayyana musabbabin kamawar gobarar ba.