An bayyana cewa, gobarar da ta kama a dazukan Amazon a watan da ya gabata ce mafi muni a cikin shekaru 14 da suka gabata.
Cibiyar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Barazil (INPE) ta shaida cewa, a binciken da aka yi da tauraron dan adam an gano gobara ta kama a wurare dubu 2,308 a dazukan Amazon.
Cibiyar ta kara da cewa, wannan adadi ya karu na sama da shekarar da a gabata da kaso 2,6 kuma tun dag 2007 zuwa yau ba a samu gobara a dazukan mai munin wannan ba.
Sanarwar da aka fitar daga Greenpeace Brazil ta ce, sauyin yanayi a lalata dazukan na Amazon ne ya ke janyo gobara a Amazon.