Giwan ruwa ya kashe wani mutum a Ostireliya

Giwan ruwa ya kashe wani mutum a Ostireliya

An sanar da cewa mutumin da giwan ruwa ya kaiwa hari a bakin tekun Cable dake yammacin kasar Ostiraliya ya mutu.

Mutumin mai shekaru 55 da aka fitar daga teku ya samu raunuka da dama sanadiyar harin da kifin giwan ruwan ya kai masa. An kuma tabbatar da cewa ya mutu nan take.

Domin daukar matakan tsaro an rufe bakin tekun, inda aka yi fadakarwa akan kar da mutane su shiga tekun.

A kasar Ostireliya dai a wannan shekarar giwayen ruwa sun kaiwa mutane hari har sau 22 daga cikinsu 8 sun haifar da rashin rayuka.

 


News Source:   ()