Rahoton Masar ga Majalisar Dinkin Duniya (UN) don girmama iyakokin ruwan Turkiyya a sanarwar kundin takardun lasisi na 18 da aka fitar ya haifar da kakkausar suka daga jaridun Girka.
Wani labari mai taken "Cin amana ta Masar" wanda aka buga a jaridar Athens Proto Thema ya bayyana shawarar da Alkahira ta yanke game da girmamam iyakokin Turkiyya kan bincike da hakar albarkatun kasa a Gabashin Tekun Bahar Rum a matsayin cin amanar tsarin aikin hukumar kasar Masar ta shekaru dubu 3.
A cikin labarin, an bayyana cewar wannan halayyar ta Masar ce ta haifar da martani daga Athens kuma Ministan Harkokin Wajen Girka, Nikos Dendias cikin gaggawa ya tattauna da Alkahira kuma bayan tattaunawarsa da Shugaban Masar Abdulfettah al-Sisi ta wayar tarho, an yi zargin cewa akwai wata takaddama tsakanin Alkahira da Athens wacce ta samo asali daga jayayya kan kamfanin da zai gudanar da binciken albarkatun kasa a yankin.
A cikin wani labari mai taken "Wasan Masar da Turkiyya" wanda aka buga a jaridar Ta Nea, an bayyana cewar gwamnatin Athens tana sa ido sosai kan bayanan yiwuwar kusancin tsakanin Turkiyya da Masar.