Hukumar Kare Hakkkokin Bil Adama ta kasa da kasa wato Human Rights Watch (HRW) ta sanar da cewa jami’an tsaron Girka na mayar da ‘yan gudun hijira zuwa cikin tekun yankin Turkiyya
A yayinda hukumar ta duba ire-iren hakan har guda tara, ta bayyana cewa a yayinda duniya ke fama da Covid-19 gwamnatin Girka ba ta dauki matakan kare yaduwar cutar tsakanin ‘yan gudun hijira ba.
An karbi bayanai daga wajen ‘yan gudun hijirar da hukumomin Girka ko kuma wasu kungiyoyi suka kora zuwa cikin tekun yankin Turkiyya.
Jaridar Daily Sabah ta rawaito cewa hukumar (HRW) ta bayyana cewa wannan matakin na Girka na korar ‘yan gudun hijira ya sabawa dokar Kare Hakkin Bil Adama ta Nahiyar Turai sakin layi na 4.