Rahotanni farko da aka samu sun bayyana cewar mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 7.5 da ta afku a yankin Oaxaca na kasar Mekziko.
Girgizar da ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 5, ta afku ne a nisan kilomita 9 daga garin Coyul na yankin Oaxaca.
Hukumar Kula da Afkuwar Girgizar Kasa ta Mekziko (SSN) ta ce bayan afkuwar girgizar mai karfin awo 7.5, an samu motsawar kasa sau 147 a cikin awanni 2.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) kuma ta ce girgizar kasar na da karfin awo 7.7, inda ta yi gargadin yiwuwar afkuwar Tsunami a kasashen Mekziko, Guatemala, Honduras da Elsalvado..