A Tsibirin Vanuatu da ke Kudancin Tekun Pasifik, girgizar kasa mai karfin awo 6,7 ta afku.
Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta sanar da cewa, da safiyar Talatar nan girgizar kasa mai karfin awo 6,7 ta afku a Port Vila Babban birnin Vanuatu.
An bayyana cewar, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 14, kuma a nisan kilomita 53 yamma da birnin Port Vila.
Ba a samu asarar rai ba sakamakon girgizar.
Haka zalika ba a bayyana yiwuwar afkuwar tsunami ba.