Mutane 5 sun rasa rayukansu a girgizar kasa mai karfin awo 5.9 da ta afku a Tajikistan.
A cikin bayanin da kwamitin bada agajin gaggawa ya yada, an rawaito cewa mutane 5 ciki har da yara sun rasa rayukansu kuma mutane 2 sun samu raunuka a girgizar kasar mai karfin awo 5.9 da ta afku a gundumar Tajikabad, kilomita 165 arewa maso gabashin Dushanbe babban birnin kasar, da safiyar Asabar din nan da misalin karfe 07:14.
A cikin sanarwar, an bayyana cewa kusan gidaje 20 ne suka lalace a yayin girgizar kuma kungiyoyin ceto suna ci gaba da aiyukan ceto a yankin da girgizar ta afku.